An Bindige Minista a Uganda, An Kashe Ƴarsa Da Mai Tsaronsa


An harbi ministan sufuri na kasar Uganda, wanda a baya ke jagorantar sojojin kasar, a wani harin da aka kai masa a ranar Talata inda aka kashe yarsa da mai tsaronsa, kamar yadda majiyar gwamnatin kasar ta sanar.

Ministan, Janar Edward Katumba Wamala, wanda ya rike mukamin babban hafsan tsaron kasar daga 2013 zuwa 2017, ya ci karo da maharan ne a Kampala, a cewar mai magana da yawun gwanati, Chris Baryomunsi.

"An yi yunkurin kashe Wamala a safiyar yau ... An bindige yarsa da mai tsaronsa kuma sun mutu nan take," Baryomunsi ya shaidawa AFP a ranar Talata.

"An garzaya da Janar Katumba zuwa asibiti da raunin harsashi a cikinsu kuma ana masa magani, masu bincike sun isa wurin da abin ya faru," ya kara da cewa.

"Akwai yiwuwar wannan kisar gilla aka yi niyyar yi amma bincike zai bayyana ainihin dalilin kai harin."

Wasu da abin ya faru a idonsu sun shaidawa gidajen talabijin na kasar cewa wasu mutane hudu da suka rufe fuskokinsu a kan babura ne suka bude wa motar Wamala wuta.

Hotuna da aka dauka sun nuna alamun yadda harsashi ya ratsa jikin motar mai lamba launin kore na gwamnatin kasar.

Harin na ranar Talata shine na baya-baya da mahara a kan babura ke kaiwa manyan mutane a babban birnin na Uganda.

A Yunin 2018, an halaka Ibrahim Abiriga, wani babban dan siyasa a jam'iyyar National Resistance Movement party a yanayi mai kama da wannan.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN