Yan bindiga sun sace shanu 500 a Masarautar Zuru jihar Kebbi


Yan bindiga, a ranar Lahadi, sun sace shanu 5000 a garuruwa daban-daban a karamar hukumar Sakaba a jihar Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar yan sakai na masarautar Zuru, John Mani, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin magana da majiyar Legit.ng a hirar wayar tarho.

Ya ce hatsabiban yan bindigan sun dade suna adabar mutanen masarautar a cikin yan makonnin baya bayan nan.

Sakaba na daya daga cikin kananan hukumomi hudu da ke masarautar Zuru a jihar ta Kebbi.

A ranar alhamis da ta gabata, yan bindiga sun halaka mutane 88 a kauyuka takwas a kananan hukumomin Danko/Wasagu.

A cewarsa, yan bindigan da suka saba kutsawa garin ta cikin jihohin Kebbi/Zamfara da iyakokin Kebbi/Niger sun kai hari a garuruwan da tsakar rana sun sace shanu da dama.

Mani ya ce babu wanda ya rasa ransa a garin sakamakon harin yan bindigan da suka zo da babura kimanin 500, kowanne dauke da fasinja daya ko biyu.


Ya ce, "Yan bindiga daga Zamfara da Niger sun kai hari wasu garuruwa a karamar hukumar Sakaba na jihar Kebbi sun sace shanu a ruga biyar.

"A kowanne ruga, akwai a kalla shanu 500. Ba su kashe kowa ba duba da cewa shanu kawai suka zo sata."

Mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, bai dauka wayarsa ba da wakilin majiyar Legit.ng ya kira shi domin jin ba'asi.

Bai kuma amnsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN