Da duminsa: Yan bindiga sun yi kaca-kaca da masarauta, sun kone gidaje sama da 60


An shiga fargaba a garin Igangan, jihar Oyo, a daren Asabar, 5 ga Yuni, yayin da wasu 'yan bindiga suka tura sama da mutane 45 zuwa kabari.

Sun News ta ruwaito cewa barnar da aka kwashe sa’o’i biyar ana yi a daya daga cikin manyan garuruwan Ibarapaland ta kai ga kone gidaje sama da 60, yayin da sama da motoci 160 kuma suka lalace.

Maharan sun yi kaca-kaca da fadar Ashigangan ta Igangan, Oba Lasisi Adeoye, da kuma wani gidan mai, yayin da suka afka wa al'ummar da misalin karfe 11 na dare.

A cewar rahoton, majiyoyi sun bayyana cewa maharan wadanda yawansu ya kai 50 a kan babura sama da 20 sun yi barna har zuwa misalin karfe 4 na safiyar ranar Lahadi, 6 ga Yuni, kafin su bar garin.

Taiwo Adeagbo, sakataren kungiyar manoma a Igangan da yake magana a kan lamarin ya ce an rasa rayuka da dama yayin barnar.

Adeagbo ya kara da cewa an harbe mazauna garin da dama, yayin da wasu jami'an tsaro suka kashe wasu daga cikin maharan.

Sunday Dare, ministan matasa da ci gaban wasanni na Najeriya yayi Allah wadai da harin da aka kai a Igangan wanda ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Dare, a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar, ya bayyana abin da ‘yan bindigan suka yi a matsayin zunzurutun mugunta, dabbanci da rashin kirki, rahoton jaridar Nigerian Tribune

Yayinda yake kira ga kwantar da hankula da zaman lafiya a tsakanin mazauna Igangan da kewaye, Ministan ya ce dole ne a kama wadanda ke da hannu cikin 'yan bindigar tare da fuskantar fushin doka.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN