Yadda aka kashe wasu iyalai Musulmai a harin ƙiyayya da aka kai musu


Rundunar 'yan sanda a Canada ta ce da "gangan" aka kashe wasu iyalai hudu Musulmai a wani hari da aka kai da mota ranar Lahadi.

An kai musu harin ne a birnin London, da ke lardin Ontario. wani yaro dan shekara tara, wanda shi kadai ne ya tsira, yana kwance a asibiti inda ya ji munanan rauni.

An tuhumi wani dan kasar Canada mai shekara 20 da laifi hudu da suka hada da kisan kai da kuma yunkurin kisa.

Harin shi ne mafi muni da aka kai wa Musulman kasar Canada tun bayan kisan mutum shida a wani masallacin birnin Quebec City a shekarar 2017.

"An yi amannar cewa an kai hari kan mutanen ne saboda su Musulmai ne," a cewar jami'in 'yan sanda Det Supt Paul Waight yayin taron manema labarai da ya gudanar ranar Litinin.

A cewarsa, 'yan sanda suna duba yiwuwar tuhumar mutumin kan laifukan ta'addanci, yana mai cewa harin na kiyayya ne.

Mene ne cikakken bayani kan batun?

Mutanen da aka kai wa hari sun hada da mata biyu - daya mai shekara 74 yayin da dayar ke da shekara 44 - da kuma namiji mai shekara 46 - da ma wata yarinya mai shekara 15.

Ba a bayyana sunayensu ba, kamar yadda iyalansu suka nemi a sakaya. Wani yaro dan shekara tara yana kwance a asibiti dauke da munanan rauni, ko da yake ba sa barazana ga rayuwarsa, in ji 'yan sanda.

'Yan sanda sun bayyana wanda ake zargi da kisan da suna Nathanial Veltman, mai shekara 20, da ke London, a lardin Ontario. An kama shi ba tare da ya yi gardama ba a wani babban kantin sayar da kayayyaki kusan kilomita shida daga wurin da ya aikata laifin.

Babu tabbas kan ko mutumin yana da alaƙa da kungiyoyin da ke nuna kiyayya, a cewar Det Supt Waight.

Masu jaje sun ajiye furanni domin nuna alhini kan kisan

ASALIN HOTON,REUTERS

Bayanan hoto


Mutane da dama da ke yankin sun kamu bisa jin labarin kisan

ASALIN HOTON,REUTERS

Bayanan hoto,

Mutane da dama da ke yankin sun kaɗu da jin labarin kisan

"Babu wata shaida da ta nuna cewa a baya akwai wata alaka tsakanin mutumin da ake zargi da aikata kisan da wadanda aka kashe," in ji Det Supt Waight, inda ya kara da cewa mutumin yana sanye da wata riga da ke nuna alamar "tana da silke".

'Yan sanda sun ce a baya ba a taba tuhumar Mr Veltman da laifuka ba.

Wata ganau ta shaida wa kafar watsa labarai ta CTV News cewa sai da ta kawar da fuskar 'yarta daga kallon gawarwakin mutanen da aka kashe.

Kazalika, wani ganau ya shaida wa CTV cewa wurin da lamarin ya faru cike yake da "hayaniya".

Kidayar da aka gudanar a 2016 ta nuna cewa London - birnin da ke da nisan kusan kilomita 200 da ke kudu maso yammacin Toronto - yana ci gaba da kasancewa mai mutanen da ke da bambance-bambancen akidu.

Akalla an haifi mutum daya cikin mutum biyar da ke zaune a yankin a wata kasa da ba Canada ba, inda Larabawa suka kasance kabilu mafiya girma a cikin tsirarun kabilun da ke zaune a yankin, sai kuma 'yan Kudancin Asia da ke biye musu.

Rahotun BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN