Yanzu yanzu: Kasuwar katako ta Umuahia na tsakar ci da wuta sakamakon rikici tsakanin yan banga da Yan kasuwaWuta na tsakar ci yanzu haka a kasuwar katako da ke kan hanyar Ahiaeke a garin Umuahia a jihar Abia.

Daily trust ta ruwaito cewa rigimar ta samo asali ne bayan wani dan kasuwa ya ki ya biya harajin N18000 da hukumar karbar kudaden harajin  jihar Abia ta sa kuma ya hana wasu yan kasuwa su biya.

Wani ganau ya gaya wa Daily trust cewa hukumar ta umarci wadanda basu biya ba su rufe shagunansu amma yan kasuwan suka ki.

Daga bisani yan bangan Abia vigilante service sun je kasuwar domin tilasta yan kasuwar su rufe shagunansu, sai dai lokacin da yan bangan suke kokarin tilasta yan kasuwa su rufe shagunansu.

Sai rigima ta kaure tsakanin wani dan banga da wani dan kasuwa da aka fi sani da suna "Indomie" sakamakon haka dan banga ya harbe shi da bindiga kum ya mutu.

Geamnatin jihar Abia ta yi Allah wadai da lamarin. Ta kuma umarci yansanda su gudanar da bincike kan lamarin domin zakulo wadanda suka kona dukiyar jama'a domin hukunta su.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN