Rundunar sojan Najeriya ta gargaɗi Sheikh Gumi kan zargin da ya yi mata


Rundunar sojan Najeriya ta bayyana kalaman Sheikh Ahmad Gumi a matsayin "abin ɓacin rai da takaici" na cewa jami'an tsaro na haɗa kai da 'yan bindiga wajen aikata laifuka.

Yayin da ya bayyana a kafar talabijin ta Arise TV ranar Laraba, malamin addinin Musuluncin ya zargi sojoji da sassauta wa 'yan fashin daji da ke addabar mazauna yankunan Najeriya.

Ya ce 'yan bindigar ba za su iya samun makamai ba ba tare da taimakon jami'an tsaron ba.

Sai dai da yake mayar da martani ga zarge-zargen, kakakin rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce kalaman "na yunƙurin ɓata sunan dakarun sojan Najeriya ne da kuma sadaukarwar da suke yi".

Ya yi kira ga manyan ƙasa da su mayar da hankali wajen nuna kishin ƙasa da kuma gina zaman lafiya "sama da zama 'yan barandan ɗaiɗaita ƙasar, abin da ka iya ta'azzara matsalar tsaron da ake fama da ita".

A cewarsa: "Yayin da rundunar soja ba za ta kare ɓata-garin cikinta ba, dole ne mu bayyana ƙarara cewa ba za ta amince da duk wani yunƙuri na zagon ƙasa ba ko kuma taimaka wa abokan gaba daga duk wani jami'inta, yayin da tuni dokoki suka tanadi hukunci".

Rahotun BBC

https://youtu.be/xRYphqBjqwc

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN