Gwamnatin Jihar Oyo ta umarci bokaye su lalubo maganin matsalar tsaro


Gwamnatin JIhar Oyo da ke kudancin Najeriya ta bai wa bokayen da ke jihar umarnin su ɗauki kowane irin mataki domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai Dr Wasiu Olatunbosun ne ya bayar da umarnin ga majalisar masu maganin gargajiya ta jihar a madadin Gwamna Seyi Makinde.

Ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ba su dukkan goyon bayan da suke buƙata domin taimakawa wajen samo maganin matsalar.

Matsalar garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa ta karaɗe kowane yanki na Najeriya, ciki har da yankin kudu maso yamma inda ƙabilar Yarabawa ke da rinjaye mai yawa.

Kazalika, yankin na fuskantar rikicin manoma da makiyaya ƙari a kan ƙungiyoyi masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya da nufin kafa ƙasar Yarabawa ta Oduduwa.

Rahotun BBC

https://youtu.be/xRYphqBjqwc

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN