Majalisar kansulolin karamar hukumar Tafa, Hon. Ibrahim Mami Ijah daga shugabancin karamar hukumar sai bayan kammala binciken kwagilolin da ya bayar ba bisa ka’ida ba. Wata takardar dakatarwa da majalisar ta fitar ranar 22 ga watan Julin nan na shekarar 2023, takardar tace dakatarwar ya biyo bayan wani zama da majalisar tayi wanda ya samu amincewar kansuloli goma na karamar hukumar, inda suka bayyana cewar sai sun kammala bincike akan zargi guda uku da su ke yiwa dakataccen shugaban karamar hukumar.
Majalisar ta zargi shugaban karamar hukumar da sayar da wani fili mallakin karamar hukumar da ke kusa da dutsen Zuma Rock akan kudi naira miliyan arba’in wanda ba su san inda aka karkatar da kudin ba. Majalisar ta zargi shugaban karamar hukumar da karkatar da kwangilar aikin hanyar Ijankoro, Ijah da aikin hanyar Sabon Bwari zuwa Aso Wusse. Haka majalisar ta zargi shugaban karamar hukumar da karkatar da kudaden bashin da ta ciwo da kudaden shigar karamar hukumar.
Majalisar kansulolin tace ta dauki matakin dakatar da shugaban karamar hukumar ne saboda kare dukiyar da jama’a suka damka a hannunsa.
Majalisar ta amince da mika ragamar tafiyar mulkin karamar hukumar ga hannun mataimakin dakataccen shugaban karamar hukumar, Hon. Muhammed Haruna.
Takardar dakatarwar da ya samu sanya hannun akawun majalisar, Enock M. Buhana da shugaban masu rinjaye na majalisar kansulolin, Hon. Idris Abdullahi.
Injiniya Kabiru Abdulhamid, wani jigo ne a jam’iyyar APC a karamar hukumar Tafan, yace duk da cewar su kan su kansulolin ba su taba gabatar da wani muhimmin kuduri da zai anfanar da jama’ar karamar hukumar ba, wannan matakin sun dauke shi ne dan bukatar kansu. Amma wani abinda ke baiwa jama’a mamaki irin kudaden da ke shigowa aljihun karamar hukumar amma watanni bakwai ke nan ba a iya biyan ‘yan siyasa albashin su na mataimaka ga shugaban karamar hukumar da sauran mukaman siyasa ba.
Rahotun Leadership Hausa
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari