Rikicin jam'iyar APC a jihar Kebbi: Dakatar da Sakataren kudin jam'iya Ali Bature bai karbu ba Inji shugaban jam'iyar Bala Sani Kangiwa


Yanzu haka wata takaddama ta taso tsakanin manyan yayan jamiyar APC mai mulki a jihar Kebbi, bayan wasu jiga jigai a jamiyar sun ayyana dakatar da Sakataren kudi na jamiyar Ali Bature ranar Asabar 6 ga watan Yuni, bisa zargin aikata ba dai dai ba.

Wata takarda da ke zagayawa a shafin sada zumunta na Facebook ya nuna cewa wasu jiga jigan jamiyar APC mai mulki a jihar Kebbi sun dakatar da Sakataren kudi na jamiyar Ali Bature daga mukaminsa.

Takardar ta yi zargin cewa ana zarginsa da aikata ba daidai ba da kudaden jamiyar, kuma aka bukaci ya bayyana a gaban Kwamiti ranar Asabar. Takardar ta ce bayan wasu awanni, sai Ali Bature ya aiko cewa manbobin Kwamitin basu da hurumin da zai yi masu bayani sakmakon haka bai je ba.

Sai dai shugaban jam'iyar APC na jihar Kebbi Arch. Bala Sani Kangiwa ya ce " Abin da ya faru matsala ce ta cikin gida kuma za mu sasanta kanmu insha Allah. Wannan dakatarwa da aka yi wa Sakataren kudi haramtacce ne kuma bai da tasiri domin ba a bi ka'idodin yinsa ba".


"Badakala  da suke zarginsa da yi wannan ba gaskiya ne ba. Ya ce basu da hurumin kiransa domin ya yi bayani saboda basu bi ka'ida ba, domin shugan jam'iya baya nan kuma shi kadai ne ke da hurumin kiran taro".

"Ya ce idan shugaban jam'iya ya kira taro zai zo ya yi bayani. Kuma kudin da suke magana cewa an bashi ba haka yake ba. Ba a bashi ko rabin adadin ba. Sakataren kudi Ali Bature tsabtatacce ne kan harkar kudin jamiya, kuma idan suna da wata hujja sai su gabatar. Kuma dakatawar da suka yi mashi bai karbu ba.

"Aje mukaminsa da Sakataren watsa labarai na jamiyar APC na jihar Kebbi ya yi, ya yi ne domin nuna bacin ransa dangane da abin da yan jamiyar suka yi ba bisa ka'ida ba. Na gaya mashi cewa ko ya kawo takardar aje mukaminsa ba zan karba ba". Inji shugaban jam'iyar APC na jihar Kebbi Bala Sani Kangiwa. 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN