A ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, Otunba Niyi Adebayo ya gabatarwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wayar hannu na farko da aka yi a Najeriya.
An gabatar da wayar ne a yayin taron Majalisar zartarwa ta Tarayya (FEC) wanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
Bugu da Æ™ari, a taron, shugaban kasar ya rantsar da kwamishinonin tarayya na Hukumar Kula da Yawan Jama'a (NPC) da Hukumar Kula da ma’aikatan Tarayya (FCSC).
Hadimin shugaban kasar a kafofin watsa labarai na zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana hakan a cikin wani wallafa da yayi a shafinsa na Facebook.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a kan wallafar:
Umar Haruna Fada ya ce:
“Wannan abin birgewa ne, muna son irin wannan rashin nasara na rantse .... Allah ya albarkaci PMB.”
Lawal Abubakar ya yi martani:“
Aiki mai kyau ya Shugaban kasa.”
Aliyu Sulaiman Idris ya ce
:“Mun yi imanin Najeriya za ta yi nasara insha Allah.”
A wani labarin, babban Bankin Duniya ya sake nazarin bunkasar tattalin arzikin da Najeriya ta yi hasashe, wanda ya kara kimanta yawan kayan cikin gida na 2021 zuwa 1.8%.
Cibiyar Bretton Wood ta daga ci gaban tattalin arzikin Najeriya daga 1.1% zuwa 1.8% na wannan shekarar, yayin da ta bayyana cewa GDP zai kara karuwa zuwa 2.1% a shekara mai zuwa, da kuma 2.4% a shekarar 2023 ta badi.
Tattalin arzikin Afirka kuwa an sake daga shi zuwa sama har 2.8% a shekarar 2021, kuma a shekara mai zuwa, tattalin arzikin yankin ana hasashen zai kai 3.3%. An kiyasta tattalin arzikin duniya cewa zai tashi da kashi 5.6%.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari