Wasu da ake zargin makiyaya ne sun yanke hannun dama na wani manomin shinkafa mai suna Saheed Zakariyau, a kauyen Bindofu dake masarautar Lafiagi, a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara, Punch ta ruwaito.
Manomin, a cewar majiyoyi, ana zargin an kai masa hari ne a gonarsa da ke kauyen Bindofu a ranar Asabar da ta gabata bayan ya zargi makiyayan da ingiza dabbobinsu wajen lalata gonarsa.
An tattaro cewa wanda manomin, tare da abokan aikinsa, ya je gonar a ranar Asabar kuma ya gano cewa makiyayan sun yi kiwon shanunsu a gonarsa tare da lalata amfanin gonar.
Rahoton da Legit ta samo ya bayyana cewa manomin da abokansa sun fatattaki makiyayan.
Sai dai, an ce daya daga cikin makiyayan ya zaro adda ya datse hannun manomin nan take.
Mai magana da yawun hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Demokradiyya da misalin karfe 1 na rana.
Ya ce, “Wani Mista Saheed Zakariyau, tare da abokan aikinsa na yankin Bindofu, Lafiagi, sun zo ofishin NSCDC, reshen Lafiagi, suka ce sun je gonarsu da misalin karfe 9:30 na safe.
"Suna zuwa wurin, sai suka tarar da garken shanu da kuma wasu Fulani makiyaya suna kiwo a gonarsu ta shinkafa.
"A yayin da suke kokarin bin Fulani makiyayan da shanunsu, wani Bafulatani ya ciro adda ya yanke masa hannun dama kuma Bafulatanin ya gudu."
Afolabi ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin tare da cafke wadanda ake zargin.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari