Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilim da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso


Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa taka hoton kwankwaso da gwamna Ganduje yayi ba dagangan bane kuma ba shiryayyen abu bane, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, shine ya faɗi haka, yace hoton da ake yaɗawa na gwamna Ganduje yana taka Fastar kwankwaso a wajen taron APC da ya gudana ranar Asabar, ba da sanin mai girma gwamna bane.

Kwamishinan ya ƙara da cewa kowane irin banbancin siyasa ke tsakanin mutanen biyu, ba halayyar gwamna Ganduje bane yayi irin wannan abun ga wani ɗan siyasa.

Yace yayin da ake cigaba da yaɗa hotunan, har wasu sun fara sukar gwamna akan lamarin saboda wata manufar su ta siyasa, lamarin zai iya zama wata babbar matsala idan ba'a fito an bayyana gaskiya ba.

Da yake bayyana ainihin abinda ya faru, kwamishinan yace:

"A lokacin taron, dandazon mabiya ɗariƙar kwankwasiyya suka sauya sheƙa zuwa APC, lokacin da aka kira gwamna yazo yayi jawabi sai waɗannan tsoffin yan kwankwasiyya suka yi layi a hanyar gwamnan domin nuna goyon bayan su ga gwamnan."

"Wasu daga cikinsu suka fara watsi da hotunan tsohon gwamnan, ɗaya daga cikin hotunan ya faɗo kan kafet din da gwamna zai taka ya wuce, ba tare da sanin Ganduje ba ya taka ya wuce."

Malam Garba yace kowa yasan gwamna Ganduje da son zaman lafiya da girmama mutane, bai kamata ace ana sukar sa kan abinda yayi bad saninsa ba.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN