Rundunar yansandan jihar Ogun ta kama wata mata yar shekara 35 mai suna Blessing Ebuneku Agoro, sakamakon sayar da yaran da ta haifa su biyu masu suna Semilore Agoro mai shekara 4, da yar uwarta Deborah Agoro mai shekara 2 akan kudi Naira 300.000.
Yansanda sun ce matar ta sayar da yaran ba tare da sanin mahaifinsu ba.
Rahotun yansanda ya nuna cewa mahaifin yaran kuma mijin matar mai suna Oluwaseyi Agoro, ya yi tafiya har tsawon shekara biyu baya gida. Bayan ya dawo ne sai matarsa ta kasa yi masa bayanin inda yaransa suke. Sakamakon haka ya kai kara wajen yansanda.
Kakakin yansanda jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ta ce matar ta yi bayanin cewa ta sayar da yaran a garin Port Harcourt a kan N300.0000 ga wasu ma'aurata wadanda ke matukar bukatar yara.
Ta ce kunci da matsanancin halin rayuwa da ta shiga bayan mijinta ya tafi ya barta da yaran har tsawon shekara biyu ya sa ta yanke shawarar sayar da yaran da ta haifa masa.
Bayanai sun ce matar tana da wasu yara biyu da ta haifa ma wani miji kafin mijinta na yanzu.
Yansanda sun kama ma'auratan da suka saye yaran, kuma suna fuskantar bincike a sashen CIID na Shelkwatar yansandan jihar Ogun.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari