Lai Mohammed ya yi magana game da sabuwar manhaja da za ta maye gurbin Twitter a Nigeria


Lai Mohammed, Ministan labarai da al'adu, ya bukaci yan Nigeria su kirkiro da shafin dandalin sada zumunta da zai maye gurbin Twitter a Nigeria.

Mohammed ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai na tarayya, a ranar Laraba 23 ga watan Yuni don kare dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi wa Twitter a cewar OAK TV.

Ministan ya karfafawa yan Nigeria gwiwa su rika kirkirar manhajarsu

Mohammed ya shawarci yan Nigeria su yi amfani da damar da ta samu bayan dakatar da Twitter su kirkiro manhajar da yan Nigeria za su rika amfani da ita.

Ministan ya ce:"

Ina ganin wannan dama ce mai kyau ga yan Nigeria masu basira su duba yadda za a yi su kirkiro manhajar da za ta maye gurbin Twitter."Ya kuma shawarci y

yanNigeria su guji amfani da VPN domin bi ta bayan gida suna shiga Twitter. Mohammed ya ce masu amfani da VPN na fuskantar hatsarin a sace musu bayanai."

Ministan ya ce:"

Shawarar da zan bawa duk wani mai amfani da VPN shine ya dena domin hakan barazana ce ga bayanan ku har da asusun ajiyar bankin ka."

Majalisa ta saka baki kan rikicin Twitter da FG

The Punch ta ruwaito cewa majalisar wakilai na tarayya ta umurci kwamitocinta na sadarwar, sharia, labarai da al'adu da tsaron kasa su yi bincike kan dakatarwar da FG ta yi wa Twitter su bada rahoto cikin kwanaki 10.

A wani labarin daban, Fadar shugaban Æ™asa ta ce gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, suna bakin ciki kan dakatar da Twitter ne saboda ya rage damar da suke da shi na yaÉ—a 'labaran Æ™arya', rahoton The Cable.

A ranar 4 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta dakatar da shafin dandalin sada zumuntan kan ikirarin cewa ana amfani da shi wurin raba kan ƴan ƙasa.

Source: Legit

https://youtu.be/xRYphqBjqwc

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN