Kaduna: Gwamna Nasir El-Rufai ya kori masu mukaman siyasa 99


Gwamnan Jihar Kaduna ya ce gwamnatin jihar ta fara aiwatar da tsarin garambawul na ma’aikatan jihar ta hanyar korar masu rike da mukaman siyasa 99.

Sai dai ya ce har yanzu fa gwamnatin jihar ba ta riga ta sallami kowane ma’aikaci ba kawai ma’aikatun gwamnatin da ke da nasaba da kananan hukumomi ne kadai suka sallami ma’aikatan.

Gwamnan wanda ya yi manema labarai bayanin hakan a ranar Alhamis ya ce wadanda aka kora daga bakin aikin sun hada da ma’aikatan kananan hukumomin jihar 23 da masu aiki a hukumar bayar da ilimin bai daya ta jihar (SUBEB) da ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko.

Ya nunar da cewa masu rike da mukaman siyasan da aka sallaman sun kai kashi 30 na adadin masu rike da mukaman siyasar a jihar.

A cewar El-Rufai

Ya zuwa yanzu masu rike da mukaman siyasa 99 ne suka rasa ayyukansu, amma har yanzu ba mu fara rage ma’aikatan gwamnatin jihar ba tukuna.

 “Muna so mu yi wa ma’aikatan adalci ne. Da farko mun yi alkawarin cewa kafin mu rage ma’aikatan jihar sai mun fara da masu rike da mukaman siyasa tukuna,”

Gwamnan ya kara da cewa dole ne a ci gaba da rage ma’aikatan kamar yadda aka tsara sakamakon kason da jihar ke samu daga rabon arzikin tarayya ya yi kasa.

A cewarsa abin da ya sa aka fara rage wa daga masu rike da mukaman siyasar shi ne dama can akwai cikakkun bayanansu a hannun gwamnatin, don haka ba za su yi wuyar tantancewa ba.

Ya ce gwamnatin ta bai wa ma’aikatan da ke kura a bayanansu damar su gaggauta zuwa gyaran bayanansu kafin a dauki wani mataki a kansu.

Sannan ya ce gwamnatin ta kuma dauki ma’aikata 11,000 a bangaren lafiya da ilimi da ma jami’ar jihar.

Ya karyata batun da ake yada wa cewa albashin masu rike da mukaman siyasa ne ke cinye kusan kudin da jihar ke samu.

A watan Maris din nan, albashin masu rike da mukaman siyasar ya kai Naira miliyan 259 yayin da na ma’aikatan ya kai Naira biliyan 3.13, ban da kudaden da gwamnatin ke bayar wa a matsayin gudummawar tara kudaden fansho da sauran harkokin gudanarwa,” inji Gwamnan.

Ya yi alkwarin cewa gwamnatin jihar ba za ta daina biyan mafi karancin albashin Naira dubu 30 da ta fara aiwatar wa.

Source: Legit Newspaper

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN