Yadda Yan daba suka kutsa cikin kotu suka fatattaki Alƙali saboda rikicin sarauta


Mutane da dama da kungiyoyi sun yi Allah wadai da kutsen da aka yi a babban kotu da ke Warri, da ake zargin ƴan ƙabilar Itsekiri magoya bayan Olu na Warri da aka zaɓa, Yarima Tsola Emiko ne suka yi a ranar Alhamis.

The Nation ta ruwaito cewa lauya mai kare hakkin bil adama, Mr Oghenejabor Ikimi ya yi tir da kutsen da ya kira gidadanci da rashin girmama kotu.

Chronicle ta ruwaito cewa 'yan daba da mata sun kutsa cikin kotun suna wakokin yaƙi inda ake sa ran fara sauran ƙarar da aka shigar na kallubalantar zaɓen Yarima Tsola Emiko a matsayin Omoba a ranar na Alhamis.

Ɗan tsohon sarkin (Olu), Ogiame Ikenwoli, Yarima Oyowoli Emiko, kawunsa, Yarima Bernard Emiko da wasu ne suka shigar da karar don kallubalantar zaɓen Yarima Tsola ɗan Ogiame Aluwatse (Olu na 19)."

Kotun na sauraren korafin ne a lokacin da hayaniyar ta ɓarke, ba a ma tsayar da ranar yin shari'ar ba kawai kowa ya watse da rikicin ya barke," wani babban lauya ya bayyana.

Jami'an yan sandan farar hula DSS ne suka fice da Alkalin kotun Jastis V. Akpoje da Cif Efe Akpofure ta kofar bayan kotun.

An gano cewar kafin a fara zaman kotun, lauyan masu shigar da ƙara Cif Akpofure SAN ya yi magana game da yiwuwar tashin hankali amma wani mai ruwa da tsaki a fadar, wanda shima lauya ne ya bashi tabbacin babu abin da zai faru.

Abin da kungiyar lauyoyi na kasa NBA ta ceK

Kungiyarlauyoyi ta Nigeria reshen Warri ta bayyana bakin cikin da mamaki "harin da wasu yan daba suka kai kotun wanda hakan yasa aka dakatar da zaman kotu a ƙarar da aka shigar na kallubalantar zaɓen Olu na masarautar Warri."

Kungiyar ta kuma yi kira ga jami'an tsaro su tsaurara tsaro a kotunan jihar domin kare sake afkuwar hakan kuma a yi bincike don gano wadanda suka kai harin don a hukunta su.

A wani labarin daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya amince da dakatar da ayyukan Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na jihar Zamfara (ZAROTA) bayan yawan koke da ake yi da ayyukan jami'an hukumar, Daily Trust ta ruwaito.

TVC News ta ruwaito cewa daga yanzu rundunar hadin gwiwa ta yan sanda, VIO, FRSC da jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ne za su rika sa ido kan ayyukan ZAROTA, a cewar sakataren dindindin na ayyukan fadar gwamnati, Yakubu Haidara.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN