Mun samu labarin shige da ficen ‘yan bindiga kafin harin makarantar Yauri – Gwamna Bagudu


Sanata Abubakar Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Kebbi, ya ce daga rahotannin da ya samu, ‘yan fashin da suka kai hari Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yauri, sun shigo a daruruwan su.

'Yan bindiga, a ranar Alhamis, sun mamaye makarantar sannan suka yi awon gaba da adadin dalibai da malamai da ba a tabbatar ba.

A wani samamen hadin gwiwa a safiyar ranar Juma'a, jami'an tsaron sun ceto wasu malamai da dalibai daga cikin wadanda aka sace, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yayin da yake jawabi ga iyayen daliban da aka sace a ranar Juma'a, Bagudu ya bayyana cewa jihar ta samu labarin shige da ficen 'yan fashi a kusa da makarantar makonni kafin harin, kuma ta tura karin jami'an tsaro.

Amma, ya lura cewa 'yan bindigar sun fi karfin jami'an, jaridar The Cable ta ruwaito.

Tunda wannan mummunan lamarin ya faru, dukkan hannaye don tabbatar da ganin cewa an ceto wadannan yaran namu da ma’aikatanmu da ransu, cikin annashuwa da kuma jin dadi.

 "Gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa ta hanyar dawo da wadannan yara da ma'aikatan lafiya," in ji shi.

Tunda wannan mummunan lamarin ya faru, dukkan hannaye sun hadu don tabbatar da ganin cewa an ceto wadannan yaran namu da ma’aikatanmu da ransu, cikin annashuwa da kuma jin dadi.

 “Wannan satar ta kasance wani lamari mai ban tsoro da takaici, inda barayin suka yi arangama da‘ yan sanda wadanda ke tsaron makarantar. Abun takaici, sun tafi da wasu dalibai da malamai. Lamari ne mara dadi.

 “Kimanin makonni biyu da suka wuce, akwai labarin shige da ficen ‘yan fashi kuma an gansu a kusa da wannan yankin. Mun tuntubi hukumomin tarayya a nan wadanda suka gaya mana cewa saura kimanin makonni biyu makarantar ta kammala jarabawarta. An amince cewa idan har za a sanya tsaro a makarantar, zai fi kyau a tallafa wa yaran su kammala jarabawarsu kafin su koma gida.”

Bagudu ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda ya tura jami’an tsaro 22 daga runduna ta musamman mai yaki da ta’addanci, kafin harin.

Sun kasance a wajen ko da aka kai harin jiya. Abin takaici, an fi karfin su, saboda baragurbin sun shigo a daruruwansu,” inji shi.

 “Wadannan yaran duk namu ne kuma ya zama wajibi a kanmu mu yi addu’a don neman dawowar su lafiya. Na yi farin ciki cewa iyayen da suka yi magana sun nuna ƙarfin zuciya.

 “Sun kuma yarda cewa jami'an tsaro sun yi iya kokarinsu kuma suna nan suna iya bakin kokarinsu, Haka kuma, hukumomin makarantar, shugaban makaranta, malamai da sauran ma'aikata. Da yardar Allah, yaranmu za su dawo gare mu."

Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC Sama da 80

A gefe guda, wasu rahotanni daga jihar Kebbi sun bayyana cewa jami'an rundunar soji sun yi gumurzu da yan bindigan da suka sace dalibai a makarantar gwamnatin tarayya dake Birnin Yauri, jihar Kebbi, inda suka hallaka aƙalla 80.

Wasu shaidu sun tabbatar wa BBC cewa sun ƙirga aƙalla gawar masu garkuwan guda 80, waɗanda sojoji suka hallaka.

Shaidun sun ƙara da cewa an yi musayar wuta sosai tsakanin jami'an rundunar soji da kuma yan bindigan.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN