Rundunar sojin saman Najeriya, ta yi amfani da jirginta na Alpha inda ta ragargaji wuraren garin Genu dake jihar Neja, lamarin da ya kawo mutuwar wasu 'yan bindiga tare da tserewar wasu.
PRNigeria ta ruwaito cewa wasu daga cikin shanun satan da 'yan bindigan suka sato daga sansanin sojoji a jihar Katsina duk sun mutu.
Daya daga cikin bama-baman ya fada wurin liyafar biki a wani kauye dake da kusanci da garin, kamar yadda ganau suka tabbatar.
Vanguard ta ruwaito yadda ganau din ke cewa, "Mun ga karamin jirgin sama yana sakin bama-bamai daga nesa da mu inda 'yan bindiga suke. Amma daya daga cikin bama-baman ya fada kauyen Argida.
"Mazauna kauyen biyu sun rasa rayukansu. Mun gano cewa wasu 'yan biki masu tarin yawa sun samu miyagun raunika.
“A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana cewa sun samu matukar nasara a luguden wutar da suka yi.
”Bamu da wani bayani na mutuwar farar hula. Burinmu da makasudin sakin bama-baman shine halaka 'yan bindigan dake yankin Genu bayan mun samu labaran sirri kan cewa sun tattaru suna son addabar jama'a."
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mulkinsa yayi kokari tun bayan da suka hau karagar a 2015.
Buhari ya sanar da hakan ne a tattaunawa ta musamman da yayi da gidan talabijin na kasa (NTA) a ranar Juma'a.
Shugaban kasan ya bukaci 'yan Najeriya da su dinga yi wa mulkinsa adalci idan suka tashi yanke hukunci. Ya kara da cewa jama'a su dinga duba abinda ya samar a mulkinsa da kuma abinda akwai kafin ya hau karagar jagorancin Najeriya.
Source: Legit.ng
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari