An gano mangwaro mai ‘fuskan mutum’ a jikin bishiya, kalli yadda jama’a sun yi tururuwan zuwa kallo a wani bidiyo


Al’umman wani gari da ba a bayyana ba sun nuna wani dan itacen mai ban al’ajabi da suka gano. Mazauna garin a cikin wani bidiyo da ya bayyana sun gano mangwaro mai kamannin fuskar mutum a jikin wani bishiya.

A wani bidiyon da @kingtundeednut ya wallafa a Instagram, an gano mutanen kewaye da bishiyan da dan itacen yake yayinda suke daukar hotuna da bidiyon.

An gano koren magwaron da launin dorawa a jikinsa.

Yan Najeriya sun yi martani kan mangwaron

Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun karbi labarin da martani mabanbanta. Wasu sun yi kokarin bayyana dalilin da yasa dan itatuwan ke da suffan mutum yayinda abun ya ba wasu mamaki.

@scoobynero ya rubuta:

Mangwaron da ya isa ci!!! Haka za su bar shi a wajen har ya nuna, ya fadi sannan ya rube.”

@therealfatfact ya ce: 

Kila ma wani ne yayi hakan da daddare Sannan shi din kuma ya kira mutane da safe don su zo su gani.”

@gabriel.ejike ya bayyana: Na shiga rudani me ya faru me yasa suke daukan mangwaron.”

A wani labarin, diyar mai kudin Najeriya, Aliko Dangote, Halima ta shiga kanen labarai kuma ta birge masu amfani da shafukan intanet.

Matashiyar matar wacce kan birge masoya da rashin hayaniyarta ta ba mutane da dama mamaki bayan ta fito ta yi rawa a wani taro da ta halarta.

Sabanin yadda aka saba ganinta, matashiyar ta sha rawa a filin taro yayinda take rera wakar da ke tashi na shahararriyar mawakiya, Teni.

Source: Legit Newspaper

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN