Tonon asiri: Gwamna Ya Bayyana Wasu Yan Siyasa Dake Samar da Motoci ga Yan Bindigan Jiharsa


Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo, yace motocin da yan bindigan suka fi amfani da su wajen kai hare-hare a jihar, wasu yan siyasa ne suka basu a lokacin zaɓen da ya gabata, kamar yadda dailynigerian ta ruwaito.

Da yake fira da gidan radio a ranar demokaraɗiyya, gwamnan yace gwamnatinsa ta fara tattara sunayen waɗan nan yan siyasan kuma bada jimawa zata bayyana wa jama'a, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A cewar gwamnan, da irin waɗannan motocin aka kai hari gidan gyaran hali dake Owerri ranar 5 ga watan Afrilu, Hedkwatar jami'an gyaran hali (NCoS), inda fursunoni da yawa suka tsere.

Mr. Uzodimma ya ƙara da cewa daga baya an samu nasarar kamo wasu daga cikin fursunonin da suka tsere.

Yace: "Mafi yawancin motocin Sienna da yan bindigan suka yi amfani da su yayin kai harin, yan siyasa ne suka samar musu lokacin yaƙin neman zaɓe, kuma suka gaza ƙwace su bayan kammala zaɓe."

"Mun haɗa sunayen waɗannan yan siyasan kuma bada jimawa ba zamu bayyana wa mutane kowa yasan su."

"Babu wata gwamnati da zata zauna tana kallo yan ta'adda su mamaye jihar ta."

A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum Aƙalla 60 a Jihar Zamfara

Wani shaida ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Alhamis, inda suka kashe mutum 54.

A cewarsa, yan bindigan sun yi awon da gaba da shanu da dama, sannan sun shiga shaguna sun ɗebi kayayyaki da yawa.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN