Yansandan jihar Osun sun kama dan shekara 40 mai suna Kabiru Oyeduntan da gundulallen sassan jikin dan Adam.
A wata takarda da Kakakin hukumar yansandan jihar ta fitar, ta ce an cafke mutumin ne sakamakon bayanan sirri da yansanda suka samu cewa wasu matsafa sun kashe wata yarinya a Unguwar Apomu ranar Alhamis 10 ga watan Yuni.
Ta ce sakamakon haka yansanda tare da taimakon yan Banga suka dira Unguwar Apomu kuma suka kama Kabiru da sassan jikin wata yarinya da ake kyautata zaton yar shekara 20 ce.
Ta ce Kabiri ya gaya ma yansanda lokacin bincike cewa wani abokinsa ne mai suna Akin ya kawo ta dakinshi dominya yi lalata da ita. Amma lokacin da ya dawo sai ya tarar cewa Akin ya kashe yarinyar kuma ya sassare sassan jikinta ya saka a cikin bokitin roba kuma ya tsere.
Ta ce yansanda za su gurfanar da Kabiru a gaban Kotu. Ta Kara da cewa yansanda sun dukufa wajen ganin sun damke abokinsa Akin da ya tsere.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari