Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin Najeriya, ya nemi sojojin da aka tura jihar Imo da su rubanya kokarinsu a yaki da haramtacciyar kungiyar IPOB a yankin kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.
Babban hafsan sojojin wanda ya yi kiran yayin da ya ziyarci sojojin ya ce ya zo jihar ne domin a tantance yanayin tsaro yadda yake a jihar.
An kai jerin hare-hare a jihar Imo a makonnin da suka gabata, ciki har da kisan wani jigon jam'iyyar APC, Ahmed Gulak.
Ana zargi haramtacciyar kungiyar IPOB da aikata hare-haren, sai dai, kungiyar ta ci gaba da musanta zargin da ake mata.
A wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samo daga Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar, ya ce babban hafsan sojojin ya kuma jinjina wa sojojin saboda juriyar su.“
Babban hafsan sojan kasa (COAS) Manjo Janar Faruk Yahaya ya yaba wa irin karfin gwiwa da kokarin sojoji na Brigade 34 da sauran jami’an tsaro wajen juya akalar rikice-rikicen rashin tsaro na baya-bayan nan wanda ya samo asali daga ayyukan ta’addanci na kungiyar IPOB, a jihar Imo."
Da yake yaba nasarorin da rundunar ta samu, ya kuma bukace su da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a yankin.
Wani yankin sanarwar na cewa:"
COAS ya nuna farin ciki kan nasarorin da sojojin suka samu ya zuwa yanzu kuma ya bukace su da su rubanya kokarin su domin karfafa nasarorinsu.
“Janar Yahaya ya kara da umartarsu da su kasance masu biyayya da nuna kwazo a kowane lokaci. Ya yi nuni da cewa, za a samu karin nasarori ta hanyar bin umarni da biyayya.
Bayan tura Burutai Benin, an tura tsoffin hafsoshin tsaro zuwa wasu kasashe
A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta sanar da tura tsoffin shugabannin rundunonin soji a matsayin jakadun Najeriya a kasashen makwabta, jaridar Cable ta ruwaito.
Gwamnatin tarayya ta sanar da tura tsoffin shugabannin rundunonin ne ta hanyar amfani da asusun sada zumunta na Koo, wani dandamali na kasar Indiya, ranar Laraba.
Saddique Abubakar, tsohon hafsan hafsoshin sojin sama, an tura shi zuwa kasar Chadi haka kuma an tura Ibok-Ete Ibas, tsohon babban hafsan sojojin ruwa zuwa kasar Ghana.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari