Ka Shirya Wa Kawo Hari Jiharka, Wata Ƙungiya Tayi Wa Gwamna Barazana Saboda Hana Kiwo


An shiga yanayin tsoro da tashin hankali a jihar Delta bisa barazanar da wata ƙungiya tayi cewa zata kai hari babban birnin jihar kan nuna goyon bayan dokar hana kiwo da gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa, yayi.

Jaridar punch ta ruwaito cewa, ƙungiyar tayi barazanar ne a wata takarda da babu sanya hannun kowa a ciki, wacce aka yi wa take da "Gargaɗin yan jihadin Fulani: buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga jihar Delta," kuma takardar na ɗauke da kwanan watan 13 ga Yuni.

Takardar wacce aka liƙa ta a wasu sassan jihar ranar Lahadi 13 ga watan Yuni, ta yi gargaɗin cewa za'a kawo hari Asaba da Agbor, jihar Delta, matuƙar gwamna ya gaza cika musu buƙatunsu nan da awanni 72.

Ƙungiyar tace:

"Muna buƙatar gwamnan Delta ya gaggauta canza matsayar da ya ɗauka kan hana makiyaya kiwo a fili wanda jihohi 17 suka amince, cikin awanni 72 daga ranar da aka rubuta wannan wasikar."

"Sannan kuma ya jiye matsayinsa na mai magana da yawun gwamnonin da suka amince da wannan dokar nan take."

Rahoton vanguard ya nuna cewa, ƙungiyar ta kira yi gwamnan da ya guje wa abun da zai biyo baya idan ya cigaba da goyon bayan hana kiwo a fili.

Ƙungiyar tace:

"Matuƙar aka gaza cika mana buƙatun mu, Jihar Delta, zata faɗa matsanancin yanayi fiye da jihohin Borno, Katsina, Kaduna, Enugu, Benuwai, Oyo, Kebbi da sauran su waɗanda suka ƙi girmama al'adun Fulani."

Hakanan kuma, ƙungiyar ta bayyana cewa tana sane da duk abubuwan dake faruwa a kudancin ƙasar nan, harda wanda aka yi a taron gwamnonin yankin kudu-kudu, kudu-gabas, da Kudu-yamma a Asaba, babban birnin Delta.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN