A wani harin bam da jirgin rundunar sojin sama ya gudanar a yankin garin Genu, jihar Neja, yayi sanadiyyar mutuwar wasu da suka halarci ɗaurin aure, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Rahoton vanguard ya nuna cewa, an kashe yan bindiga da dama yayin wannan aiki na jirgin NAF
Rahotanni sun bayyana cewa harin da jirgin yaƙin ya kai ya kashe wasu makiyaya dake aikin satar shanu, kuma jirgin ya taso ne daga sansanin soji dake jihar Katsina.
Sai dai an gano cewa ɗaya daga cikin bam ɗin da jirgin ya jefa ya dira a wurin taron murnar ɗaurin aure a Wani Ƙauyen jihar Neja, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya tabbatar.
Shaidan yace: "Mun hangi wani jirgi na sakin bam a maɓoyar yan bindiga, amma ɗaya daga cikin bam ɗin ya sauka a wurin taron murnar ɗaura aure a ƙauyen Argida."
"Biyu daga cikin mazauna ƙauyen sun mutu, kuma mun gano cewa wasu baƙi da aka gayyato wajen taron sun ji raunuka."
Amma da aka tuntuɓi kakakin rundunar sojin sama, Edward Gabkwet, yace harin bam ɗin da suka gudanar ya tafi yadda ake so cikin nasara.
Yace: "Ba a kawo mana wani rahoton cewa harin ya shafi waɗanda ba ruwan su ba, manufar mu ita ce yan bindigan dake yankin Genu. Bayan mun samu rahoton fasaha cewa sun taru a yankin suna ƙulla shirin kaiwa mutane hari."
Source: Legit.ng
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari