J
ama'ar garuruwan Magami da Mayaɓa a ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara a arewacin Najeriya, na can su na ci gaba da makoki bayan kisan gillar da 'yan fashin daji suka yi wa mutane a cikin gonakinsu.
Da yammacin ranar Laraba, wani shaida ya ce sun yi wa mutum goma sha bakwai, jana'iza kuma an raunata ƙarin manoma tara, baya ga dabbobi da suka yi awon gaba da su.
Manoman na tsaka da aikin share gonakinsu lokacin da maharan suka auka musu.
Wani da ya tsallake rijiya da baya a harin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa sun yi jana'izar mutanen da aka hallaka.
Sannan Æ´an bindiga sun wawushe musu dukiya da dabobbi. Kuma babu jami'in tsaro lokacin da aka kai musu harin.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin SP Muhammad Shehu, jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sandan jihar Zamfara, sai dai haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.
Rahotun BBC
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari