An kama malaman makaranta bisa zargin ya wa dalibinta duka har ya mutu a Kano


Hukumomi a karamar hukumar Fagge a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce sun rufe wata makaranta sakamakon zargin cewa dukan da wata malama ta yi wa wani ɗalibi ne ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Iyayen marigayi Surajo Surajo Isa sun yi zargin cewa malamar makarantar El-Salam Success Acadamy da ke unguwar Kurna ta yi wa yaron nasu dukan da ya yi ajalinsa.

Tuni rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wacce ake zargin don gudanar da bincike.

Mahaifiyar ɗalibin ɗan shekara tara Hajiya Salma, ta shaida wa BBC cewa ɗan nata lafiya ƙalau ya tafi makaranta a ranar Talata, sai kawai aka kawo mata shi ranga-ranga wai ba shi da lafiya, inda ta ce nan take suka garzaya da shi zuwa asibiti.

Taƙara da cewa "Da na kai shi asibiti likita ƙin taɓa min shi ya yi ya ce wannan yaron me aka yi masa, sai na ce malamarsa ce ta ce kansa na ciwo sai na je na ɗauke shi.

"Sai likita ya ce 'a'a wallahi ya wuce faɗuwa, tun da ga wani abun nan yana ta ɓulɓula ta hancinsa, ga jini ga kumfa.'

"Haka na haƙura na koma makarantar na same ta amma ta dinga cewa ita ba za ta bi ni ba don ba ta san me ya same shi ba. Sai wasu ƴan uwanta malamai biyu da suke wajen suka dinga kakkare ta wai ba abin da ya samu Surajo.

"Na fashe da kuka na fita zan koma asibitin shi ne suka biyo ni muka tafi asibitin, kafin na ƙarasa Allah Ya karɓi rayuwarsa.," a cewar mahaifiyar yaron.

Alhaji Ibrahim Muhammad Abdullahi shi ne shugaban karamar hukumar Fagge, ya ce bayan samun rahoton mutuwar ɗalibin, sai ya bayar da umarnin a rufe makarantar don a sami damar gudanar da bincike.

"Na ba da umarnin rufe makarantar ne saboda hargitsi da yake neman ya faru. Da daddare ma sai da na zauna da dattijan unguwa da matasa da dama wadanda suka taso ana so a ƙona makarantar.

"Ni kuma na ga ba makarantar kawai abin zai shafa ba har ma da gidajen da ke kusa da ita. Dole na sa aka rufe aka kuma tura ƴan sanda suka kwana a wajen," a cewarsa.

Mista Sunday Daniel shi ne mai makarantar ta el-Salam Success Academy, ya kuma cewa BBC daga binciken da ya gudanar kawo yanzu ba duka ne ya kashe yaron ba.

Sai dai ya ce yana fata binciken da 'yan sanda suke yi zai fito da haƙiƙanin abin da ya auku.

"Makarantar ba a dukan yara, akwai dokoki na hana duka da azabtarwa. Kuma duk tambayoyin da na yi wa ma'aikata da yaran makarantar sun ce ba duka aka yi wa yaron ba," in ji Mista Daniel.

"Yanzu dai za mu jiran sakamakon ƴan sanda tun da wannan zargi mutanen da ke waje ba su san abin da ke faruwa a makaranta ba su ne suka yaɗa shi."

A nata bangaren rundunar 'yan sandan jihar Kano tuni ta kama wacce ake zargi da dukan wannan yaro.

Mai magana da yawun rundunar DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce sun duƙufa don gano abin da ya faru.

"Mun je mun gayyato malamar da shugabannin makarantar da ƴan uwan yaron da tuni aka yi wa jana'iza.

"Kwamishinan ƴan sanda ya sa an mayar da ƙorafin babban sashen binciken manyan laifuka da ke Bompai, ɓangaren kisan kai. Yanzu haka an gurfana don binciken lamarin," in ji DSP Kiyawa.

Mahaifiyar marigayi Surajo ta ce tun a baya ma ɗan nata yana yawan kai mata ƙorafin cewa malamar tana dukansa, amma sai ta yi buris da ƙorafin saboda a cewarta wataƙila ƙorafi ne irin na ƙin zuwa makaranta.

Rahotun BBC

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN