Yan bindigan sun farmaki Kano sun yi luguden wuta sun sace attajiri


Miyagun 'yan ta'adda da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai farmaki jihar Kano kuma sun tasa keyar wani attajirin dan kasuwa dake karamar hukumar Dambatta a jihar.

'Yan bindigan sun kai farmakin garin Kore a tsakar daren Alhamis inda suka dinga ruwan wuta babu sassauci, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan mummunan hari yana zuwa ne bayan kwana daya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yayi korafin cewa miyagu sun fara tattaruwa a dajin Falgore dake jihar Kano.

Legit.ng ta ruwaito yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci hukumomi da su yi hanzarin tarwatsa miyagun dake tattaruwa a dajikan Kano kafin al'amuransu su yi karfi.

Kamar yadda mazauna garin suka sanar, hantarsu ta kada sosai ganin masu harin sun shiga cikin gari a babura suna ruwan wuta, al'amarin da yasa mazauna yankin fadawa dajika cikin dare.

Sun sanar da cewa basu samu daukin jami'an tsaro ba koda aka kai farmakin, hakan yasa suka tasa keyar wani attajirin dan kasuwa a garin.

Mazauna garin sun sanar da cewa ba a yi asarar rai ko daya ba, sai dai wani karamin yaro ya samu rauni sakamakon harbin bindiga a kunne.

Muhammad Abdullahi Kore, shugaban karamar hukumar Dambatta ta jihar Kano ya tabbatar da satar attajirin dan kasuwar.

Rahotun legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN