Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi


Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar Muhammad daga kan karagar sarauta saboda zargin hannu a ayyukan ‘yan bindiga a masarautarsa.

Dakatarwar na zuwa ne bayan harin ranar Alhamis da ‘yan bindigar suka kai a kauyen Kadawa da ke masarautar inda suka kashe mutum 90.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mukaddashin Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take kuma an nada Alhaji Bello Suleiman (Bunun Kanwa) a zaman wanda zai tafiyar da al’amuran masarautar.

A cewar Sakataren, Gwamnan jihar, Bello Mohammed Matawalle, MON, shi ne ya bada umarnin dakatar da basaraken tare da nadin wanda zai jagoranci kafin a kammala bincikar sarkin.

Ya kara da cewa, gwamnan ya kuma amince da kafa wani kwamitin mutum tara da zai binciki Zange-zargen da ake yi wa basaraken na hannu a yaduwar hare-haren ‘yan bindigar a masarautar Zurmin.

Kwamitin wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar, Malam Ibrahim Wakkala jagoranta yana da wakilcin jami’an tsaro guda uku da sauran mambobin biyar, an ba shi wa’adin mako uku da ya mika rahoton bincikensa.

Sarkin Zurmi, ya zama basaraken gargajiya na uku da gwamnatin jihar ta dakatar kan zargin su da hannu a aika-aikar ‘yan bindiga a cikin Jihar Zamfara.

A baya gwamnatin ta dakatar da Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar da Hakimin Nasarawa Mailayi, Alhaji Bello Kiyawa.

Source: Legit Nigeria

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN