Zargin kama mutane a motar Hilux dauke da bindigogi a Masarautar Zuru kuskure ne- Rahotun gaggawa


Ta tabbata cewa zancen kama wata sabuwar mota kirar Hilux dauke da bindigogi kirar AK47 guda 5 tare da wasu mutane a yankin Senchi da ke Masarautar Zuru a jihar Kebbi ranar Juma'a 30 ga watan Aprilu kuskure ne. 

Mun samo daga wata majiya ta tsaro a jihar Kebbi cewa, ranar 30 ga watan Aprilu wasu jami'an safiyo (Surveyors) ma'aikatar sashen man petur na kasa NNPC suka isa yankin Senchi a Masarautar Zuru domin gudanar da aikin saka tuta da ke nuna GBS bisa aikinsu na safiyo a daji da ke kewaye da rikon Senchi. Amma sai suka gamu da turjiya daga wasu mutanen yakin sakamakon wani kuskuren rashin sanar da su da kuma Uban kasar Senchi zancen zuwansu da aikin da ya kawo su.

Mun samo cewa tun farko, tawagar ta sanar da Fadar Mai martaba Sarkin Zuru isowarsu Masarautar Zuru da kuma bukatar gudanar da ayyukansu kafin ranar 30 ga watan Aprilu.

Kazalika bayanai sun tabbatar cewa bindigogi kirar AK47 da ake zargin an samu a motar Hilux na jami'an tsaron da ke yi wa ma'aikatan rakiya ne watau Escort, kamar yadda aka saba a bisa tsarin tafiyar da irin wannan aiki.

Lamari da ke nuna cewa kuskure ne zancen da ke ta yawatawa a WhatsApp dauke da muryar tattaunawar wayar salula tsakanin wasu mutane guda biyu dangane da lamarin da ke zargin motar da jama'a da ke cikinta da wata boyayyar manufar tsaro.

Tuni Masarautar Zuru ta daidaita lamarin kuma komi ya koma dai dai bisa tsarin doka da oda kamar yadda aka saba.

Ana kyautata zaton jami'an za su koma yankin domin ci gaba da aikin da ya kawo su mako mai zuwa, bayan sun kammala muhimmin aikin sanar da duk wanda ke da hakkin sanin bayyanarsu domin gudanar da aikinsu a yankin.



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN