Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko


Mambobin ƙungiyar Boko Haram sun ƙwace iko da gonaki da kuma ayyukan gona a garin Geidam, jihar Yobe kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan, waɗanda suka kori mafi yawancin mutanen garin, sun fara yiwa mutanen da suka rage wa'azi akan jihadi, sannan kuma suna basu kyautar kuɗi.

Gambo Abdullahi, wani ɗan asalin garin Geidam dake zama a Damaturu, yace har yanzun garin na hannun yan ta'adda yayin da sojojin Najeriya na can yammacin garin.

Yace: "Har yanzun yan Boko Haram na cikin Geidam, kuma su keda ikon gudanarwa a garin. Tunda suka kori mutanen garin, sun cigaba da yin wa'azi kan tsattsauran ra'ayin jihadi ga mutanen da suka rage."

"Bayan sun kammala wa'azin su, suna bayar da kuɗi N20,000 domin su jawo hankalin mutanen su shigo ƙungiyarsu."

"Hakanan kuma yan ta'addan sun kwace iko da gonakin mutane, Kuma sun fara gyaran gonakin ta hanyar cire ciyawa da sauransu, kai kace zasu daɗe ne a garin."

A wata majiyar daga Damaturu babban birnin jihar, Muhammed Sale, yace wasu daga cikin mutanen da suka rage a garin sun fara guduwa zuwa ƙauyen Kalgeri ɗake kusa da Geidam ɗin.

Yace: "Ba'a hada-hadar abin hawa zuwa garin Geidam, duk wani abun hawa a Kalgeri yake tsayawa, iyayena sun baro Geidam zuwa Damaturu, saida suka yi tafiyar kafa mai tsawo zuwa Kalgeri sannan suka sami mota zuwa Damaturu."

A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan da yan bindiga keyiwa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire na Jihar.

Gwamnatin tace yan bindigar na haka ne don kawai su jawo hankalinta ta canza matsayarta na 'Ba biyan kuɗin fansa' da kuma 'Ba maganar sulhu da yan bindiga'

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN