Za'a yi dokar da za ta bawa Mata damar auren Miji fiye da daya a Afirka ta Kudu


Kamar yadda aka yarda da auren mace fiye da daya a wasu kasashen, wata sabuwar dokar aure a Afirka ta Kudu na iya bawa mace damar auren fiye da miji daya kwanan nan.

Dokar na daya daga cikin wadda aka fi nuna bukata a wata takardar jin ra'ayoyin mutane akan dokar aure.

An fitar da kundin dokoki mai shafuka 67 wanda sashen kula da al'amuran zamantakewa ya fitar a satin nan.

Sashen a cikin kundin ya karfafa cewa ana so a kirkiri sabuwar dokar aure a kasar don rushe na halattattun aure da aka sani

Dokar auren Hindu, Yahudawa, Musulmi da Rastafariya duk basa cikin dokokin Afirka ta Kudu, a daya bangaren kuma ana ganin cewa dokar auren ba za ta samar da daidaito ba. An kara wannan cikin takardar neman jin ra'ayin.

"Rashin sanya auren wadannan addinai bai dace ba kuma ba abin aminta bane," a cewar kundin.

Takardar jin ra'ayin ta samar da nau'ikan aure uku don samar da daidaito a dokokin aure.

Doka ta farko ta bada damar auren gargajiya da na addinai, wanda zai bada damar gudanar da shagulgula ba tare da la'akari da banbancin launin fata ko kabila ko addinai ba.

Zabi na biyu zai bada damar aure irin na addini wanda ba zai shafi al'ada ba.

Zabi na uku zai zama wanda zai bada damar auren mace fiye da daya ga namiji ko namiji fiye da daya ga mace, a cewar kundin.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN