Da duminsa: Barayi sun kai hari Aso Rock, sun shiga gidan nakusa da Buhari


Labari da duminsa na nuna cewa wasu barayi sun yi yunkurin fasawa cikin gidan shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, dake Aso Rock, birnin tarayya Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Litinin.

Garba ya bayyana cewa barayin basu samu nasarar satan komai ba.

"Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya tabbatar da cewa an yi "wawan yunkurin" yi masa fashi a gidans misalin karfe 3 na daren nan amma basu samu nasara ba," Garba Shehu yace.

"Farfesa Gambari...ya ce babu wani abin damuwa."

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN