Jami'an rundunar yansandan jihar Bauchi sun kama wani matum dan shekara 34 mai suna Lamido Gunduma bisa zargin kashe budurwarsa mai juna biyu tare da Jaririnta a karamar hukumar Jama'are.
Kakakin hukumar yansandan jihar Bauchi ASP Ahmed Wakil ya shaida wa manema labarai ranar Juma'a 14 ga watan Mayu. Ya ce wanda aka kama ya hada baki tare da abokinsa domin su zubar da cikin gaba da Fatiha da ya dirka wa budurwarsa yar shekara 35 mai suna Jamila Sa'idu, amma sai Jamila ta mutu yayin kokarin zubar mata da cikin.
Ya ce bayan mahaifin Jamila mai suna Sa'idu Iliyasu ya kai kara wajen yansanda ranar 7 ga watan Mayu da karfe 12 na rana.
Yansanda sun gano gawar Jamila a magudanar ruwa tare da jinjirin da ta haifa a gidan saurayinta Lamido a Unguwar Yari-mani da ke garin Jama'are. Yansanda sun gurfanar da Lamido gaban Alkalin Kotu.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka