An gano gawar matashi rataye har ya mutu a wani shago da ke gaban ofishin yansanda


An gano gawar wani matashi rataye da igiya har ya mutu a wani shago da ke gaban ofishin yansanda na Okota ranar Asabar 15 ga watan Mayu.

Rahotanni sun ce an gan saurayin a Unguwar da misalin karfe 10 na dare yana tambayar wani Mai indomi ranar Juma'a. Kwatsam sai aka gan gawarshi a cikin shagon ranar Asabar da misalin karfe 8 na safe.

Mabanbantan ra'ayin jama'a ya yi zangin cewa Yan sanda sun tsare babur da yake tukawa ne. Wasu kuma suke zargin cewa watakila wasu ne suka kashe yaron sai suka zo suka rataye gawarsa a nan.


Wata majiya ta ce yansanda sun je wajen da lamarin ya faru da motar daukar gawa Ambulans, sai dai sun tafi ba tare da sun saukar da gawar ba. Lamari da ake tunanin za su dawo ne da ayarin Kwararrun yansanda da suke da hurumin binciken kwakwaf kan irin wadanan matsaloli.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN