Sarkin Bauchi, Rilwanu Sulaiman Adamu, ya dakatar da Wakilin Birnin Bauchi, Yakubu Shehu Abdullahi, a kan rashin da'a ga sarki da kuma shigar alfarmar da yayi tamkar Sarki yayin hawan Sallah.
Masarautar tace Abdullahi, wanda dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Bauchi a tarayya karkashin jam'iyyar PRP, an dade ana jan masa kunne a kan rashin da'a ga sarki da masarautar amma yayi kunnen kashi.
A wata wasika mai kwanan wata 16 ga Mayun 2021 wacce aka aika ga dan majalisar a harshen Hausa, masarautar tace shigar da yayi a Alkyabba da Kandiri a gaban sarki ba al'amari bane na da'a.
"Masarautar karkashin shugabancin Sarkin Bauchi, ta duba ayyukanka wanda ta ga rashin da'a ne ga Sarki, shugabannin siyasa, 'yan majalisar sarki, hakimai da sarakuna.
“Masarautar ta bada misali da yadda ka bayyana gaban Sarakuna da Alkyabba da Kandiri duk da an ja maka kunne a kan hakan.
“Abinda ya faru a ranar Asabar, 15 ga watan Mayun 2021 a gidan gwamnati ya nuna yadda baka da'a ga Sarki, masu sarauta da gwamna.
"A saboda haka, masarautar ta dakatar da kai daga sarautar Wakilin Birnin Bauchi har sai baba ta gani," wasikar tace.
Source: Legit.ng
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka