Kebbi: Bayan sun sha ruwan duwatsu, Jami'in tsaro ya sheke saurayi a garin Babarejo


Wani saurayi ya rasa ransa bayan jami'in tsaro ya bindige shi har lahira sakamakon hatsaniya da ta barke tsakanin jami'an tsaron border drill a garin Babarejo da ke rikon garin Dakingari a karamar hukumar Suru da ke Masarautar Gwandu a jihar Kebbi ta tsakiya ranar Asabar 7 ga watan Mayu.

Shafin labarai na ISYAKU.COM ya samo cewa rigima ta barke ne da misalin karfe 12 na ranar Asabar a garin Babarejo lokacin da jami'an tsaro na hadin gwiwa da ke sa ido kan harkar fasakwabri suka yi kokarin binciken wasu kayaki a garin Babarejo, amma sai hatsaniya ta kaure.

Wata majiya mai tushe a garin Babarejo ta shaida mana cewa 

" Jami'an Kwastam sun zo ne daga shelkwatarsu suka nemi wucewa zuwa garin Babarejo cikin motocinsu guda biyu. Amma sai matasa kimanin 100 suka datse hanya suka sa shinge kuma suka kunna wuta".

"Garin Babarejo yana cikin Fadama ne, saboda haka hanya daya ce ta shiga garin kuma ita ce za a bi a fito. Sakamakon haka ya zama da wuya jami'an su wuce a wanan yanayi".

"Na jiyo cewa jami'an Kwastam sun je ne domin su kama wasu buhunan takin zamani da aka shigo Naneriya da su ba bisa ka'ida ba. Amma sai wasu matasa suka hana.  Daga bisani masu kayan sun zo suka sami jami'an. Sarkin Yamma Babarejo ya je ya yi wa matasan bayani tare da bukatar matasa su bari jami'an su yi aikinsu. Sun aminta sun bari jami'an suka wuce suka shiga Babarejo".

"Sai dai bayan Sarkin Yamma ya wuce. Kwastam sun shiga Babarejo suka kama buhu 35 na haramtaccen takin zamani da aka shigo da su kuma a gaban masu takin ba tare da wata matsala ba".

"Lokacin da jami'an ke kan hanyar komawa sai suka tarar cewa samarin sun sake datse hanyar, sun banka wuta kuma suna ta jifan jami'an da duwatsu suna ihu suna cewa bamu yarda ba. A cikin wannan hatsaniya ne aka jefi wani jami'in da dutse har sai da ya fadi a kasa".

"Bayan ya tashi ne kawai cikin rudani sai ya yi harbi da bindiga. Wanda daga bisani harsashin ya sami wani saurayi kuma ya sami rauni. An kai saurayin zuwa Asibiti a garin Dakin gari. Sai dai bayan Sallar La'asar sai aka sami labarin rasuwar saurayi wanda dan asalin garin Dakin gari ne ba dan garin Babarejo bane".

Border drill ta kunshi jami'an tsaro daga yansanda, soji, kwastam da sauransu. Sai dai mutuwar saurayin ya sa jijiyoyin wuyar matasan garin Babarejo ya tashi.

Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce " Muna sane da faruwar lamarin, sai dai yanzu haka DPO na Dakingari na gudanar da bincike kan hakikanin abin da ya faru a wajen kafin a mika lamarin zuwa sashen SCIID a Shelkwatar hukumar yansandan jihar Kebbi".

ISYAKU.COM ya samo cewa kura ta lafa kuma jama'a sun ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda aka saba a garin Babarejo kawo yanzu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN