Gwamna ya yiwa El-Rufai wankin babban bargo, ya ce yana daya daga cikin makiyan Najeriya na hakika


Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana takwaransa na Kaduna a matsayin daya daga cikin makiyan Najeriya.

Gwamna Ortom ya yi wannan ikirarin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Terver Akase ya aika wa Legit.ng a ranar Asabar, 8 ga watan Mayu.

Gwamnan na Benuwai yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da aka alakanta da El-Rufai wanda ya zargi Ortom da amfani da rashin tsaro a jiharsa wajen kai hari ga gwamnatin tarayya.

Gwamnan na Kaduna ya ci gaba da cewa, Ortom yana amfani da dabaru ne domin rufe abin da ya kira gazawar gwamnan jihar Benuwai.

Sanarwar ta bayyana cewa harin da El-Rufai ya kaiwa Gwamna Ortom don kawai yayi farin jini ne a gaban fadar shugaban kasa.

Gwamna Ortom ya kara zargin El-Rufai da inganta rashin tsaro a kasar ta hanyar kalaman sa.

Wani bangare na jawabin ya ce:

“Nasir el-Rufai mashahuri ne, gwarzon kabilanci, kuma mai tsananin son addini wanda yake kin duk wanda ba addinin shi daya da shi ba. Yana cikin yan tsirarun mutanen da suka batar da Shugaba Muhammadu Buhari.

"El-Rufai na daya daga cikin makiyan kasar nan na hakika wadanda ba sa boye bambancin ra'ayinsu ta hanyar fifita son zuciya da kabilanci sama da kyawawan dabi'u da suka hada Najeriya a tsawon shekarun da suka gabata."

A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shawarci yankin kudu maso gabas da su nemi takarar shugaban kasa ta hanyar siyasa, maimakon yin barazanar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, El-Rufai ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, a wani taro ta shafin yanar gizo da kungiyar Shugabancin Afirka ta shirya.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN