Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, amma dai a duba: Kwamitin duban wata


Kwamitin duban wata na majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya ta sanar da cewa ganin jinjirin watan Shawwal ranar Talata, 29 ga watan Ramadana da kamar wuya.

A bayanin da kwamitin tayi ranar Asabar a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa an yi hasashen ko wata ya bayyana zai fito ne gabanin faduwar rana, saboda haka ba zai yiwu a ga jinjirin wata ranar Talata a Najeriya ba.

Amma duk da haka jama'ar Musulmi a fadin Najeriya su fita neman jinjirin wata saboda yin hakan ibada ne.

Ranar Talata, 11 ga Mayu ya yi daidai da 29 ga watan Ramadana da ake fara neman jinjirin watan Shawwal na shekarar 1442AH.

Wani sashen jawabin yace: "A ranar Talata, 29 ga Ramadana 1442AH (11 ga Mayu, 2021).. Tun da haihuwar jinjirin ba zai faru faru ba kuma wata zai fadi gabanin rana, hakan na nuna cewa ba zai yiwu a ga wata a Najeriya ranar Talata 11 ga Mayu, 2021 ba.

"Amma dai a sani cewa neman wata kowace ranar 29 ga wata ibada ne."

"Saboda haka a nemi wata ranar Talata."

Kwamitin ta kara da cewa duk wanda yayi ikirarin ganin wata, wajibi ne ya bada gamsasshen bayanin yadda ya gani.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN