Gwamnan Ondo Zai Buɗe Sabon Masallaci Na Farko da Aka Gina a Cikin Gidan Gwamnatin Jiharsa


Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, yace buɗe sabon masallaci a cikin gidan gwamnatin jihar ranar 4 ga watan Yuni zai zama ɗaya daga cikin ayyukan da zaiyi alfahari dasu a bikin cikarsa kwana 100 a kan mulki.

Mr Akeredolu, wanda aka sake zaɓensa a karo na biyu, yace za'a sanya wa masallacin sunan tsohon shugaban hukumar kula da walwalar musulmai ta jihar, Khalid Fawehinmi, wanda ya rasu a shekarar 2020.

Gwamnan ya faɗi haka ne a ranar lahadi yayin da ya karɓi baƙuncin Shugabannin musulmai na jihar a wajen buɗe baki a ɗakin taro na ƙasa-da-ƙasa dake Akure.

Gwamnan yace: "Gwamnatin mu itace ta farko data gina masallaci a cikin gidan gwamnati, kuma ina mai tabbatar muku da cewa ba zan nuna banbanci a tsaƙanin addinai ba."

"Zamu sanya wa masallacin sunan tsohon shugaban hukumar kula da walwalar musulmai ta jihar, Khalid Fawehinmi,"

"Ina kira ga mabiya addinin musulunci da kuma kiristanci da su zauna lafiya a tsakanin su, domin duka addinan biyu suna koyar da son juna da kuma sadaukarwa."

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa zata bada muhimmanci ga cancantar mutum bawai daga wane addini ya fito ba.

Shugaban hukumar kula da walwalar musulmai, Zikrullah Chandy, ya yabawa gwamnan bisa soyayyar da yake nunawa musulmai a faɗin jihar.

Ya kuma jinjinawa gwamnan bisa wannan namijin ƙoƙari da yayi na gina masallaci a cikin gidan gwamnati domin musulmai dake wajen su rinƙa ibada.

A wani labarin kuma Jami'an Soji Sun Damƙe Mayaƙan Boko Haram 10 a Jihar Kano

Sojoji sun yi ram da wasu mutane da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ta'addaci ta Boko Haram ne a cikin garin Kano ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 10 ne suka shiga hannu lokacin da suka yi ƙoƙarin kai hari wani masallaci a yankin Hotoro.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN