Abubuwan da ya kamata ka sani game da Zakkar Fidda Kai, Tare da Sheikh Aminu Daurawa


Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malamin ya yi bayanin cikin sauki abubuwan da ya kamata mutum ya sani game da Zakkatul Fitr (Zakkar fidda kai)

ZAKKAR FIDDA KAI

Wannan wata sadaka ce da ake kira zakkar fidda kai, sadaka ce da ake yi idan an Æ™are azumin watan Ramdhan, kafin a yi sallah Idi.

Malamai sun faÉ—i hikimomin da ke cikin wannan sadaka.

Na farko: Tana tsarkake mai azumi daga zunuban da ya aikata da bakinsa yayin azumi.

Na biyu: YaÆ™i ne da yunwa da kuma kyautatawa talakawa, kamar yadda hadisi ya zo daga Manzon Allah ï·º, ana samun lada mai yawa a wannan sadaka, kamar yadda Manzon Allah ï·º ya ke cewa; “Wanda ya bayar da wannan sadaka kafin a tafi sallar idi, Allah ï·» zai karva masa. Wanda kuma ya bayar bayan an dawo daga sallar idi ta zama sadaka ce kamar sauran sadakoki.” Ibn Maja ne ya raiwato shi.

Sannan sadaka ce da ke nuna godiyarka ga Allah ï·» da ya raya ka har Shekara ta zagayo kana lafiya.

ZAKKAR FIDDA KAI TANA DA SHARAÆŠI HUÆŠU

Na farko: Mai bayarwa ya zamo Musulmi.

Na biyu: Ya kasance mawadaci.

Na uku: Ya zamo an ba da ita a kan lokaci.

Na huÉ—u: A bada ita ga wanda ya cancanta.

WAÆŠANDA ZAKKAR FIDDA KAI TA ZAMA WAJIBI A KANSU

Wannan zakka tana zama wajiba a kan kowani Musulmi babba da yaro, mace da namiji, tsoho da tsohuwa, É—a da bawa.

MATAKAN DA AKE BI WAJEN FITAR DA ZAKKAR FIDDA KAI GUDA UKU NE

Ya halatta a bayar da ita kafin zuwan ranar Idi da kwana É—aya ko biyu.

Lokacin fitar da zakkar fidda kai yana farawa ne daga faÉ—uwar ranar ashirin da tara (29 ga watan Ramadan zuwa kafin a tafi sallar Idi.

An so a fitar da wannan zakka ranar SAllah kafin a tafi Idi. Ba ya halatta a jinkirta ta har sai an dawo Idi.

Zakkar fidda kai ana bayar da ita ne gwargwadon kwano É—aya, wato mudannabi huÉ—u kenan.

NAU'IN ABINCIN DA AKE BAYARWA

A zakkar fidda kai ana bayar da kowani nau'in abincin da mutanen garin suke amfani da shi, kamar dangin su alkama, shinkafa, gero, dawa, masara, da wake. Amma an fi so a bayar da abin da mutum zai iya sarrafawa ya ci cikin sauƙi, kamar shinkafa, alkama ko filawa.

WAÆŠANDA AKE BA ZAKKAR FIDDA KAI SU NE TALAKAWA DA MISKINAI

Wasu malaman suna ganin ya halatta a zakkar fidda kai mutum ya bayar da kuɗi maimakon abinci, amma idan wanda za a ba ya fi buƙatar kuɗin, wataƙil wani ya ba shi abincin amma ba kuɗin dafawa.

Wajibi ne idan ka fitar wa kanka zakkar fidda kai, sai kuma ka fitar wa da ‘ya‘yanka da matarka da waÉ—anda ke Æ™arÆ™ashinka idan ba su da hali.

Zakkar fidda kai ana bayar da ita ne a garin da ake zaune sai dai idan duka garin masu arziƙi ne shi ne za a iya fitar da ita wani garin daban.

Source: Legit Newspaper


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN