Yadda aka kama dan shekara 30 da ke yi wa jama'a fyade a Sokoto


Jami'an hukumar tsaro ta Civil Defence reshen jihar Sokoto ta ce ta kama wani da ake zargi ya kware wurin fyade da cin zarafin yara a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito cewa Hamza Yusuf, dan shekara 30 da ake zargin ya ci zarafin yara 10 amma uku cikinsu kadai aka gano kawo yanzu.

A yayin jawabin da ya yi wa manema labarai, kwamandan NSCDC na jihar, Umar Musa Bala ya ce dukkan wadanda abin ya shafa ba su kai shekara 10 ba.

Ya ce an ceto wanda ake zargin ne a daidai lokacin da fusatattun mutane suka shirin halaka shi.

"An kira mu an sanar da mu cewa an kama wani da ake zargin mai fyade ne kuma za a halaka shi a Mabera, nan take muka bazama muka tafi.

"Mun ceto shi daga hannun wadanda ke shirin halaka shi muka kawo shi ofishin mu.

"Mun iya gano uku cikin wadanda ya ci zarafinsu kuma likitoci sun tabbatar da hakan sannan dukkansu shekarunsu bai kai 10 ba," in ji shi.

Bala ya kara da cewa za a bada belin wanda ake zargin saboda yajin aikin da ma'aikatan shari'a ke yi amma za a saka tsararan dokoki a belin.

"Dole sai ya kawo wanda zai tsaya masa wanda zai zama sananne ne a garin kuma zai iya kawo shi a duk lokaci da ake bukata," in ji shi.

Ya kuma yi kira ga iyaye su rika sa ido a kan yaransu domin laifin ya zama ruwa dare.

Wanda ake zargin ya amsa cewa ya aikata laifin yana mai cewa shaidan ne ya rinjaye shi amma ya yi alkawarin ba zai sake ba.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN