Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri


Mayakan kungiyar Boko Haram sun cinna wuta a wasu a gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Ana kuma jin karar harbin bindiga da abubuwa masu fashewa a sassan birnin daban-daban musamman kusa da Jiddari Polo.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa ana musayar wuta tsakanin sojoji da wasu da ake zargin yan ta'adda ne a kusa da Molai da Jiddari a babban birnin jihar.

"An ji a kalla karar abin fashewa uku a Maiduguri. Ana harbe-harben bindiga a halin yanzu, farar hula suna tserewa daga gidajensu suna tafiya hanyar Damboa da tsohuwar GRA," a cewar majiyar tsaro.

Wani mazaunin garin da ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce bashi da wurin zuwa a halin yanzu saboda halin da ake ciki.

"A yanzu babu inda zan iya tafiya. Ba zan iya zuwa gida ba. Kana iya jin karar harbin bindigan?" in ji shi.

'Yan ta'addan sun kai harin ne a daidai lokacin da musulmi ke shirin yin bude baki a cikin watan Ramadan mai albarka.

Daga bisani, zaratan dakarun sojoji sun fatattake yan ta'addan amma a halin yanzu ba a kiyasta adadin barnar da yan ta'addan suka yi ba.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN