Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Wani matashi ya sha dukan ajali a hannun makwabta da jama'an gari, duba dalili


Wani mutum da ake zargin dan fashi ne mai suna Emmanuel ya sha dukan ajali a hannun jama'a ranar Lahadi 16 ga watan Mayu.

An dade ana zargin wanda aka kashe da addaban jama'a a garin Ayede-Ogbese da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo. 

Wata majiya ta ce an taba daure Emmanuel a Kurkuku bisa laifin fashi. Sai dai bayan an sako shi sakamakon kammala wa'adin zaman gidan kaso sai ya dawo ya ci gaba da abin da ya saba.

Sakamakon haka jama'a suka sa ido a kan harkokinsa. Dubun Emmanuel ta cika ne ranar Lahadi 16 ga watan Mayu bayan motar da ta dauko masa babura da ya kwace a hannun mutane guda 4 ta lalace.

Mutanen gari sun kama shi suka yi masa dan Karen duka, sai dai yayin da yansanda ke kan hanyarsu ta kai shi Asibiti sai ya mutu a hanya. 

Kakakin hukumar yansandan jihar DSP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yayin da yansanda ke kan hanyar kai Emmanuel Assibiti sai ya mutu kafin a isa Asibiti domin jama'a sun riga sun yi masa mumunan duka.

Ya bukaci jama'a su guji daukar doka a hannusu. 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies