Yan bindiga da ake kyautata zaton yan ta'addan Independent People of Biafra (IPOB) ne sun sheke yansanda biyu suka banka wa ofishin yansanda wuta a a jihar Abia.
Tsagerun sun farmaki ofishin yansanda na Apumiri Ubakala da ke karamar hukumar Umuahia ta kudu da sanyin safiyar ranar Litinin. Ofishin yansandan yana cikin shahararren kasuwar Ubakala.
Wani dansanda ya gaya wa Daily trust cewa kafin farmakin ranar Litinin kan ofishin yansandan, Shelkwatar yansandan jihar ta sami rahotannin sirri cewa akwai yiwuwar za a farmaki ofishin na yansanda.
Ya ce rahotun ya ba da shawarar cewa ko dai a tsaurara tsaro a ofishin, ko a rufe ofishin na wucin gadi. Ya ce ba a yi ko da daya daga cikin shawarar da aka bayar ba.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka