Ƴan sanda a Uganda sun ce sun kama wani da ake zargi da safarar yara ƙanana yana tsafi da sassan jikinsu.
BBC ta naɗi mutumin a wani binciken ƙwaƙwaf da ta yi a shekarar 2011.
An kama mutumin da ake zargi, wani direban babbar mota, a garin Elegu da ke iyakar arewacin Uganda a ƙarshen makon nan.
Mai magana da yawun ƴan sanda Fred Enanga ya tabbatar da cewa za a miƙa mutumin ga hedikwatar ƴansanda a Kampala, babban birnin kasar.
Ya ce ƴan sanda sun san da ayyukan mutumin ne bayan da wani bidiyo da aka naɗa shekara 10 da ya wuce, ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka nuna mutumin yana cewa shi ne shugaban wata ƙungiya mai sace yara su mika su ga ƴan kungiyar asiri.
A wani rahoto, mutumin da ake zargi ya yi wa tawagar BBC da suka yi ɓadda kama bayani kan yadda za su iya samun yaran sata.
Mista Enanga ya ce ƴan sanda za su yi bitar zarge-zargen sannan yana kira ga duk wani wanda yake da bayani dangane da lamarin ya taimaka.
Har zuwa wannan watan, dokokin Uganda ba su sa amfani da sassan jikin mutum a matsayin babban laifi ba.
A farkon watan nan ne majalisar dokoki ta sa hannu kan wani ƙudirin doka wadda idan aka sa wa hannu za ta ba da damar yanke hukuncin kisa ga wanda aka kama yana amfani da sassan jikin mutum ko taimakawa wajen amfani da su.
Rahotun BBC Hausa
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari