Da duminsa: Rundunar soji ta sauyawa Operation Lafiya Dole suna


Rundunar sojin Najeriya ta sauyawa rundunar Operation Lafiya Dole dake yakar Boko Haram suna zuwa Operation Hadin kai.

Wannan ne suna na uku da aka sanyawa rundunar tun bayan kafa ta.

Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai a 2015 ya sauya mata suna daga Operation Zaman Lafiya suwa Operation Lafiya Dole, wanda yace hakan yayi shi ne domin tabbatar da cewa dole ne a samu zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

Amma Mohammed Yerima, mai magana da yawun rundunar, a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, yace sauya sunan zuwa hadin Kai na nufin zama tsintsiya daya.

Hakan yana daga cikin kokarin Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasan, na ganin an kakkabe duk wani rashin hadin kai dake wurin kuma a samar da aiki cike da kwarewa.

"Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru, ya amince da sauya suna Operation Lafiya dole zuwa Operation Hadin kai," takardar tace.

“An yi hakan ne saboda tsabar cigaban da rundunar sojin kasar ta samu a shekarun da suka gabata kuma saboda a tabbatar da hakan."

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa tace Ejike Mbaka, shugaban Adoration Ministry (AMEN), ya taba kawai shugaban kasa 'yan kwangila uku amma aka dakatar da shi.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace Mbaka ya makance da har ya bukaci shugaban kasa ya yi murabus sakamakon tsanantar matsalar tsaro a kasar nan.

A wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, Shehu yace akwai matukar abun mamaki ta yadda wanda ya goyi bayan shugaban kasan har sau biyu a yau ya sauya ya koma yana neman yayi murabus ko a tsige shi.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN