Da duminsa: Fusatattun yan acaba sun farmaki ofishin FRSC a garin Zuru sun kone tahuna, duba dalili


Rundunar yansandan jihar Kebbi da ke garin Zuru ta dakile tashin hankali da ya bijiro sakamakon buge wani dan achaba da wata mota ta yi a shingen binciken motoci da jami'an hukumar FRSC suka yi a garin Zuru ranar Litinin.

Rahotanni daga garin Zuru sun ce da safiyar ranar Litinin jami'an FRSC suka tare ababen hawa domin bincikensu a kusa da kofar shiga Jami'ar koyon aikin gona da ke garin Zuru a kudancin jihar Kebbi.

Mun samo cewa bayan tare wani babur ne ke da wuya, sai wata mota da ke tafe a baya ta zo da gudu ta buge babur da ke wajen shingen jami'an FRSC, sakamakon haka matuki babur ya fadi kwance a kasa ya sami rauni.


Sai dai majiyarmu ta ce bayan labari ya kai cikin garin Zuru, sai yan acaba kimanin 200 suka fusata suka nufi ofishin FRSC kuma suka yi ta zage zage har da jifa da duwatsu. Sakamakon wannan rudani aka banka wa tahunan wutar lantarki na ofishin wuta.

Majiyarmu ta ce nan take jami'an yansanda suka iso ofishin na FRSC kumu suka harba barkonon tsohuwa sau uku, nan take jama'a suka watse daga wajen da gudu.

Sai dai mun samo cewa bayan da kura ta lafa, wani jami'in FRSC ya gamu da fushin yan acaba a Unguwar Rikoto shiyar tashar mota, bayan yan acaba sun bi shi suka yi masa dan karen duka, har sai da jami'in ya ruga ya shiga wani gida domin ceton ransa.

Mun samo cewa nan take yansanda sun dira Unguwar Rikoto, kuma suka ceto jami'in FRSC daga hannun fusatattun yan acaban da suka ja daga a kofar gidan da jami'in ya shiga ya sami mafaka.


Mun tattaro cewa an kai jami'an FRSC biyu da aka raunata zuwa Asibiti, sai dai an yi zargin cewa, har ila yau, yan acaban sun je har Asibiti domin daukar fansa. Sai dai bayanai sun ce jami'an tsaro sun bayar da cikakken kariya kuma ana zargin an dauke jami'an na FRSC an kai su Asibitin cikin barikin soji domin samun kulawan Likita.

Jami'an hukumar FRSC da suka sami raunuka sun hada da Mahmud Inusa da Sunday Adamu suna samun kulawan Likita tare da wadanda motar ta buge.

Mun tattaro cewa ba rayuwar da ta salwanta a wannan hargitsin. Kazalika jami'an tsaro basu yi amfani da harsashi ba a kan kowa a wannan matsalar.

Tuni yansanda suka shawo kan lamarin. Kura ta lafa kuma jama'a na ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba a garin Zuru.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN