Yan Bindiga Sun Kashe Kwamishina, Sun Sace Shugaban Ƙaramar Hukuma a Kogi


Yan bindiga sun kashe kwamishina a hukumar Fansho ta jihar Kogi, Mr Solomon Akeweje sannan sun sace shugaban karamar hukumar Yagba ta Yamma, Mr Pius Kolawole, The Nation ta ruwaito.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP William Aya, ya tabbatar da hakan inda kwamishinan da Kolawole suna cikin mota daya ne a yayin da yan bindigan suka kai musu hari.

Ya ce yan sanda sun samu rahoton kai harin misalin karfe 4.30 na yamma a ranar Asabar 1 ga watan Mayu kuma nan take suka garzaya inda abin ya faru.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce an kaiwa wadanda abin ya faru da su hari ne a Eruku, wani gari da ke kan iyakan jihar Kwara da Kogi.

A cewar Iya, Akeweje da Kolawole suna hanyarsu ta komawa Egba ne daga jihar Kwara inda yan bindigan da ba san ko su wanene ba suka kai musu hari.

Ba a san inda Kolawole da aka sace ba yake a halin yanzu kuma wadanda suka sace shi ba su tuntubi kowa ba.

Amma, direban motar ya tsira da ransa yayin da aka kai gawar Akeweje asibitin ECWA da ke Egbe.


A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN