Bidiyon fasto tana yi wa 'yan cocinta tofin Allah tsine a kan sun ki tara mata kudin bikin bazday


Wata fasto ta yi tofin Allah tsine ga mambobin cocinta sakamakon kin tara mata kudin shagalin murnar bikin zagayowar ranar haihuwarta da suka yi.

A wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an ji faston tana kiran mambobin cocinta da shaidanu saboda kin yi mata wannan kara da suka yi.

"Ko a ranar zagayowar haihuwata, wasu daga cikinku sun ki bada kudi. Ubangiji zai ladabtar da ku saboda baku da tausayi, sai dai kuma idan baku da kudin."

"Ba wai kamar kudin nawa bane, na abincin da zaku zo ku ci ne. Wasu daga cikinku mugun ci garesu kamar aladu kuma sai kun kwasa wani abincin kun tafi da shi gida," faston tace.

Ga bidiyon nan mai karatu ya kalla a kasa:

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, ta musanta rade-radin da ake yi na cewa mayakan Boko Haram sun kai farmaki babban birnin kasar Najeriya.

Ana ta yadawa cewa Boko Haram sun kai hari Abuja bayan samun su da aka yi a jihar Neja dake makwabtaka da su, The Cable ta ruwaito.

Yusuf Mariam, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, ta ce an ga jama'a masu yawa a babura a wasu sassan babban birnin tarayyan, lamarin da ya kawo wannan rade-radin kuma yasa jami'ansu suna fita sintiri.

A wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi, Mariam tace an fara tsananta sintiri kuma hakan yana daga cikin matsayar da aka cimmawa bayan taron hadin guiwa na jami'an tsaro da aka yi a ranar Alhamis.

Source: legit News


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN