Gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar kwadagon Najeriya NLC sun yi yarjejeniya kan shirin sallamar ma'aikata kimanin 7000 da gwamnatin El-Rufa'i ke shirin yi.
Tun ranar Litnin NLC ta fara zanga-zanga da yajin aiki kan abinda gwamnatin jihar tayi.
Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta shirya zaman sulhu tsakanin bangarorin biyu a Abuja.
PT ta rahoto cewa daga cikin yarjejeniyar da sukayi shine gwamnatin Kaduna ta cigaba da muradinta amma ta bi dokokin kwadago na korar ma'aikata bisa sashe na 20 na dokar kwadago.
Hakazalika sun yarje cewa NLC ba zata cigaba da yajin aikin ba amma kuma kada gwamnatin jihar ta hukunta duk wani ma'aikacin gwamnatin jihar da ya shiga yajin aikin.
Zaku tuna cewa gwamnatin Kaduna ta sanar da sallamar malaman jinya da malaman jami'ar KASU da suka shiga yajin aikin. Wannan yarjejeniyar ta rusa wannan hukunci.
Bayan haka an kafa kwamitin mutum 10; mutum 6 daga bangaren gwamnatin Kaduna, 3 daga bangaren NLC, da kuma mutum 1 daga bangaren gwamnatin tarayya domin tattauna yadda za'a wanzar da yarejejeniyar.
Dukkan bangarorin biyu sun rattafa hannu kan wannan yarjejeniya.
Source: Legit.ng
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari